Resumen del episodio
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...
Episodios
Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar
EscuchadoMahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...
Ra'ayoyin masu saurare kan kawo ƙarshen wasa da Argentina da Messi yayi
EscuchadoRa'ayoyin masu saurare kan wasan ƙarshe da Ɗan wasa Lionel Messi ya bugawa ƙasarsa. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Dan Bauchi.
Ra'ayoyin masu saurare kan fatan ci gaba da haƙo man fetur a wasu sassan arewacin Najeriya
EscuchadoTaron gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya gudana a ƙarshen mako, ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta farfaɗo da aikin binciken man fetur da aka faro tsawon shekaru a yankin. Kazalika taron ya buƙaci gwamnatin da ta mayar da hankali wajen gyara layin dogon da ya haɗa biranen Port-court-Jos-Bauchi-Gombe zuwa Maiduguri saboda muhimmancinsa wajen buƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙarancin makamashi a wasu ƙasashen yammacin Afrika
EscuchadoYayin da kusan a kowane mako ana iya a wayi gari da sabon farashin man fetur a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar ana fama da ƙaranci da kuma tsadarsa ne a wasu jihohin ƙasar, yayin da ake fama da gagarumar matsalar ƙarancin gaz da ake amfani da shi domin girki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta
EscuchadoYau juma'a kamar yadda aka saba, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...